Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tinubu ya nada sabon shugaban EFCC

Published

on

Shugaban Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya nada Mista Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC.

Mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kai na shugaban kasar, Ajuri Ngelale ne ya bayyana hakan a wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis.

Nadin Olukoyede ya biyo bayan murabus din Shugaban Hukumar, Abdulrasheed Bawa bayan dakatar da shi da akayi.

Tinubu ya kuma amince da nadin Muhammad Hassan Hammajoda a matsayin sakataren hukumar yaki da cin hanci da rashawa na tsawon shekaru biyar, kafin majalisar dattawa ta tabbatar da su.

Shugaba Tinubu ya bukaci sabbin shugabannin Hukumar da su tabbatar da sun yi aiki tukuru, don tabbatar da dakile cin hanci da rashawa a Kasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!