Connect with us

Labarai

Najeriya da Kamaru sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaron jiragen sama

Published

on

Najeriya da Kamaru sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da nufin ƙarfafa tsaro da inganta harkokin sufurin jiragen sama tsakanin ƙasashen biyu.

 

Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama da Bunƙasa Sararin Samaniya na Najeriya, Festus Keyamo, ne ya sanya hannu a madadin Najeriya, yayin da takwaransa na Kamaru, Ministan Sufuri Jean Ernest NgalNgallé Bibehe, ya sanya hannu a madadin ƙasarsa.

 

An gudanar da bikin rattaba hannun kan yarjejeniyar ne a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, inda bangarorin biyu suka jaddada aniyarsu ta haɗa kai domin tabbatar da tsaro, inganta musayar bayanai, da bunƙasa zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Najeriya da Kamaru.

 

Ana sa ran yarjejeniyar za ta taimaka wajen daidaita ƙa’idoji, rage haɗurran jiragen sama, da kuma ƙarfafa alaƙar diflomasiyya da tattalin arziƙi tsakanin ƙasashen biyu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!