Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Najeriya da sauran ƙasashen afurka sun yi asarar dala biliyan 190 sanadiyar Korona – Adesina

Published

on

Shugaban bankin raya ƙasashen afurka, Dr. Akinwumi Adesina, ya ce, tattalin arzikin nahiyar afurka, ya yi asarar dala biliyan casa’in (190), sakamakon ɓullar cutar korona.

Mista Adesina ya bayyana hakan ne yayin taron shekara-shekara da bankin ya saba gudanarwa, wanda aka yi na wannan shekara ta kafar internet.

Ya ce, ɓullar cutar ta covid-19 ya janyo al’ummar nahiyar sama da miliyan talatin faɗawa cikin ƙangin talauci.

‘‘Yanzu haka ƙididdiga da muka gudanar mun gano cewa mutane miliyan talatin da tara, ka iya faɗawa cikin ƙangin talauci a wannan shekara matukar ba a ɗauki mataki ba’’ a cewar Adesina.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!