Labarai
Najeriya na cikin kasashe goma da suka fi cin bashi a duniya – Bankin duniya
Bankin duniya ya ce, Najeriya na cikin jerin kasashe goma da suka fi cin bashi a duniya.
Cikin wata sanarwa da bankin ya fitar a Larabar nan ya ce, bashin da yake bin Najeriya ya kai sama da dala biliyan 8 da miliyan 656.
Bankin ya kuma ce ƙasar India ita ce ke kan gaba da bashin dala biliyan 22 sai ƙasar Bangladesh da ake bin ta dala biliyan 11 da miliyan 7, yayin da Pakistan ake bin ta dala biliyan 16 da miliyan 4.
Sauran kasashen sune: Vietnam da ake bin ta dala biliyan 14 da miliyan daya, sai Ethiopia dala biliyan 11 da miliyan 2, sai ƙasar Kenya da ake bin ta dala biliyan 10 da miliyan 2.
Bankin duniyar ya ce, ƙasar Tanzania ana bin ta bashin dala biliyan 8 da miliyan 3 sai Ghana dala biliyan 5 da miliyan 6, yayin da Uganda ke da bashin dala biliyan 4 da miliyan 4 kamar yadda sanarwar ta bayyana.
You must be logged in to post a comment Login