Labarai
Najeriya na rasa fiye da Dala biliyan 56 duk shekara- Kashim Shettima

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa Najeriya ta na rasa fiye da dala biliyan hamsin da shida a duk shekara sakamakon matsalar rashin abinci mai gina jiki.
Shettima ya ce wannan matsala tana dakile ci gaban ƙasa, tana ƙara yawaitar talauci, tare da lalata ƙwarewa da damar da ‘yan ƙasa za su iya amfani da ita wajen raya tattalin arzikin ƙasa.
Ya kara da cewa, idan aka kula da batun abinci mai gina jiki da muhimmanci, hakan zai taimaka wajen inganta lafiya, rage talauci, da kuma gina ƙasa mai ƙarfi da ci gaba.
Kashim Shettima ya yi wannan bayani ne yayin wani taro na musamman da aka shirya domin tattauna hanyoyin magance matsalar rashin abinci mai gina jiki a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login