Connect with us

Labarai

Najeriya ta gargadi ‘yan ƙasar a kan shiga yake-yake a wasu kasashen

Published

on

Najeriya ta gargadi ‘yan ƙasarta a kan shiga yake-yake a wasu kasashen bayan wani rahoto da ya fito da ke cewa an yaudari wasu ‘yan kasar inda suka shiga yakin da Rasha ta ke yi a Ukraine.

 

Cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta fitar, ta bayyana matukar damuwarta a kan yadda ake kara samun ‘yan Najeriya da ake dauka aiki ba bisa ka’ida ba domin su je su yi yaƙi a wasu kasashen.

 

Rahoton wanda aka wallafa a makon da ya gabata wanda wasu masu bincike suka gudanar kan sojojin haya na Rasha, ya ce rundunar sojin Rasha ta dauki ‘yan Najerya akalla 36 aiki domin su yi yaki a Ukraine inda aka kashe mutum biyar daga cikinsu.

 

Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta ce,”Yawancin ‘yan Najeriyar da aka dauka irin wannan aiki an tura su fagen daga bayan an yaudaresu da cewa za a ba su aiki a rundunar sojin Rasha.”

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!