Labarai
Najeriya ta motsa a matakin na 148 zuwa na 104 kan ayyukan cin hanci da rashawa a duniya
Kasar nan ta motsa gaba daga mataki na dari da arba’in da takwas zuwa na dari da arba’in da hudu a rahoton da kungiya mai rajin yaki da cin hanci da rashawa ta kasa da kasa Transparency International ta fitar na wannan shekara kan ayyukan cin hanci da rashawa a duniya.
A cikin rahoton na Transparency International ya kuma ce kasar Amurka ta samu koma baya, inda ta bar matsayin da ta ke na goma sha takwas a shekarar da ta wuce zuwa na ashirin da biyu.
Sai dai rahoton ya ce kodayake Najeriyar ta samu ci gaba amma ba ta samu Karin maki ba kan ashirin da bakwai da ta samu a shekarar da ta wuce.
A cewar rahoton na Transparency International dai, Najeriya ta yi kan-kan-kan da kasashen Kenya da tsibirin Comoros da Guatemala da kuma Mauritania a matsayi na dari da arba’in da hudu, wanda hakan ke nuna cewa akwai sassaucin ayyukan cin hanci da rashawa a kasashen fiye da kasar Kamaru wadda ta ke matsayi na hamsin da biyu a duniya.
Kasar Bostwana ce dai kasa ta daya a nahiyar afurka, inda aka fi samun karancin cin hanci da rashawa a cewar rahoton na Transparency International wadda kuma ita ce ta Talatin da hudu a duniya, sai kasashen Namibia da Mauritius da kuma Senengal wadanda su ke biye ma ta baya, cikin kasashen Afurka da ake samun karancin cin hanci da rashawa.
Rahoton na Transparency International ya kuma ce kasar Denmark ce akafi samun karancin cin hanci da rashawa a duniya sai kuma kasar New Zealand da ta ke bi ye ma ta a baya, yayin da kasashen Somalia da Syria da kuma Sudan-ta-Kudu suka kasance kasashe da aka fi samun cin hanci da rashawa a duniya.