Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Rashawa : EFCC ta hukunta musu laifi fiye da 600 a Najeriya

Published

on

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce a shekarar 2020 ta  hannun kotu ta hukunta masu laifi dari shida da sittin da biyar daga cikin kararraki dubu daya da dari uku da biyar da ta shigar gaban kotuna.

Mukaddashin shugaban hukumar ta EFCC, Mohammed Abba ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren.

Muhammad Abba ya kuma ce yanzu haka ana ci gaba da gudanar da bincike kan kararraki dubu bakwai da dari uku da Arba’in daga cikin kararraki dubu goma da dari da hamsin da biyu da aka shigar gaban hukumar.

Ya kuma ce hukumar ta kuma gano makudan kudade tare kwace wasu kadarori da dama daga mutanen da ake zargi da cin hanci da rashawa a kasar nan.

Sanarwar ta ce shugaban rikon na EFCC ya kuma godewa ma’aikatan hukumar kan irin kokarin da su ke yi na aiki tare da sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukansu, wanda hakan ya taimaka wajen samun nasarar da aka samu a shekarar ta 2020.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!