Connect with us

Labarai

Najeriya ta samu rarar kasuwancin waje ta dala biliyan 4.6

Published

on

Babban Bankin kasar nan, CBN, ya sanar da cewa ƙasar nan ta samu rarar kuɗaɗen mu’amalar kasuwanci da ƙasashen waje da ya kai dala biliyan 4 da digo 60 a zangon uku na shekarar 2025 da mu ka yi bankwana da ita.

 

Rahoton da bankin ya fitar ya nuna cewa wannan ci gaba ya biyo bayan koma bayan da aka samu a zangon da ya gabata, inda aka danganta sauyin da karuwar ribar asusun kasuwanci na yanzu zuwa dala biliyan 3 da digo 42, tare da ƙarfuwar kuɗaɗen da ‘yan Najeriya ke turawa daga ƙasashen waje, da kuma ƙaruwa a harkokin kuɗi.

 

Ta cikin wata sanarwar da Hakima Sidi Ali, Darakta mai riƙon kwarya ta sashen sadarwar bangaren kamfanoni na Babban Bankin kasar nan ta fitar ta ce, wannan sakamako na zangon uku na 2025 na nuna ƙarfuwar tattalin arziƙin waje, da ƙarin kwarin gwiwar masu zuba jari, tare da tasirin gyare-gyaren da ake aiwatarwa a kasuwar musayar kuɗi da manufofin kuɗi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!