Kiwon Lafiya
Najeriya tana bukatar naira tiriliyan daya don yaki da zazzabin cizon sauro – Ministan lafiya
Gwamnatin tarayya ta ce tana bukatar jimillar naira tiriliyan daya da biliyan tamanin da tara don yaki da cutar zazzabin cizon sauro.
Ministan lafiya Dr. Osagie Ehanire shine ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a birnin tarayya Abuja, a wani bangare na bikin ranar yaki da cutar malaria a duniya na wannan shekara.
Ya ce matukar Najeriya na bukatar cimma manufar ta na rage adadin mutanen da ke mutuwa sanadiyar cutar zazzabin cizon sauro daga nan zuwa shekarar dubu biyu da ashirin da biyar, to kuwa akwai bukatar fitar da makudan kudade don cimma wannan nasara.
Dr Osagide Ehanire ya kuma ce, gwamnatin tarayya ta fitar da wani taswira da ta tsara da manufofi ta shekaru biyar da nufin yakar cutar zazzabin cizon sauro a Najeriya.
You must be logged in to post a comment Login