Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kaso 24 cikin 100 na wadanda ke mutuwa sakamakon zazzabin cizon sauro ‘yan Najeriya ne

Published

on

Kwamishinan lafiya na jihar Ogun Dr. Tomi Coker, ya ce, kashi 24 cikin dari na mutanen da ke mutuwa a duniya sanadiyar cutar zazzabin cizon sauro ‘yan Najeriya ne

 

Dr Coker ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai a garin Abeokuta babban birnin jihar ta Ogun a wani bangare na bikin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro na duniya da ke gudana a ranar lahadi.

 

Ya ce wannan kididdiga ce da hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta yi game da mace-macen da ke faruwa a duniya sanadiyar cutar malaria

 

Ya ce abu daya da za ayi don magance matsalar shine a ci gaba da raba gidajen sauro mai magani wanda zai taimaka gaya wajen kare mata masu juna biyu da kuma yara ‘yan kasa da shekaru 5.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!