Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Najeriya za ta karbi jirage samfurin Super Tucano a watan Yuli – Buhari

Published

on

Gwamanatin tarayya ta ce Najeriya za ta karbi jiragen sama shida daga cikin jiragen yaki 12 samfurin Super Tucanos a watan Yulin 2021 wanda shi ne kasaon farko don kawo karshen ayyukan masu ta’addanci a kasar nan.

Babban hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

Ya ce, sauran jiragen shidan zasu karaso kasar nan jim kadan bayan isowar saitin farko, kuma za a horas da matukan jiragen 14 a sansanin soji da ke Georgia a Amurka.

Jaragen Super Tucanos dai an kera su a Florida, kuma yanzu haka ana ba su horon fara aiki don tabbatar da ingancin su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!