Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

Ana wata ga wata: Mutane 135 sun kamu da cutar corona a ranar alhamis a Najeriya

Published

on

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta ce akalla mutane dari da talatin da biyar sun kamu da cutar covid-19 a ranar alhamis.

A cikin wani sako da cibiyar ta NCDC ta fitar a shafinta na twitter a daren jiya alhamis, ta ce, sai dai ba a samu rasa rai ba sanadiyar cutar ta corona.

Wannan adadi dai bai kai na ranar laraba da ta gabata ba, wanda mutane 187 suka kamu da cutar.

Rahotanni sun ce mutane dari da talatin da biyar din sun fito ne daga wasu jihohi goma sha shida na kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!