Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Nan ba da jimawa ba zan fasa ƙwai – Muhyi Magaji

Published

on

Tsohon shugaban hukumar Anti Kwarafshin ta jihar Kano Muhyi Magaji Rimin Gado, ya ce zai yi bankaɗa kan wasu al’amuran Gwamnatin Kano.

Rimin Gado ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da Freedom Radio.

A cewar sa takun saƙar da ta sanya aka dakatar da shi daga shugabancin hukumar bai wuce yadda yaƙi amincewa a yi almundahanar wasu kuɗaɗe ba.

“Lokacin da aka dakatar da ni daga hukumar, kuɗin da nake da shi bai wuce naira dubu saba’in da uku ba, kuma a ranar da za a kore ni sai da na samo kuɗaɗen da aka iya aiwatar da hukumar kafin na bar ofishin”.

“Ni bana tsoron binciken da ake yi a kaina, domin kuwa babu tsoron wani abu da nake, duba da yadda na san ina da tarin shaidu da hujjoji a kan zargin da aka ce ana yi min” a cewar Muhyi.

Daga nan ya ƙara da cewa, “Duk wasu abubuwa da kuka sani ina da kwafi domin su zamar mun shaida, in ba don haka ba, ban isa na zo na yi wannan hirar ba, kuma tuhuma ta da ake yi taɓa mutunci na ne, domin kuwa babu wanda bai san ina zuwa ganin likita ba”.

A baya-bayanan dai Gwamnatin Kano ta sauke Muhyi daga mukamin sa, wanda a yanzu ake gudanar da bincike bisa zarge-zargen da aka yi masa a lokacin da yake shugabantar hukumar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!