Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Nan ba da jimawa ba zan sanar da matsaya kan tsayawa takarar shugaban ƙasa –Kauran Bauchi

Published

on

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammed, ya ce, nan ba da jimawa ba, zai sanar da matakin da ya ɗauka kan ko zai tsaya takarar shugaban ƙasa ko akasin haka a zaɓen da za a gudanar a shekarar 2023.

Gwamnan na Bauchi ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke tattaunawa da wata ƙungiyar matasan ƙasar nan waɗanda suka kai masa ziyara fadar gwamnatin jihar Bauchi.

‘‘Ina tabbatar muku cewa zan zauna in nazarci buƙatar da kuka zo mini da ita, zan kuma tuntuɓi waɗanda ya kamata in tuntuɓa, musamman al’ummar mazaɓata wato jihar Bauuchi, ƴan jaridu, ƴan majalisa na jiha dana tarayya, tsofaffin ma’aikatan gwamnati, gwamnonin jam’iyyar PDP da dattawan jihar Bauchi da kuma na jam’iyyar ta mu ta PDP’’ a cewar gwamna Bala Muhammed.

Da ya ke miƙa takardar gayyatar ga gwamnan na Bauchi, shugaban ƙungiyar Elliot Afiyo, ya ce, salon mulki na gari da gwamnan ke yi ga jihar sa, ya sa suka ga dacewar gayyatar sa da ya jagorancin ƙasar nan.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!