Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Nan ba jimawa ba za mu fara biyan ma’aikatan shara haƙƙinsu – Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce, nan ba da jimawa ba za ta biyan ma’aikatam sharar titi albashin da suke bin tsohuwar gwamnatin Gandujea.

Haka kuma gwamnatin ta ce, za ta kawo ƙarshen matsalolin da ma’aikatan shara ke fuskanta na rashin albashi tsawon lokaci.

Kwamishinan muhalli Nasiru Sule Garo shi ne ya tabbatar da hakan a zantawar sa da manema labarai.

Nasir Garo, tuni aikin tattara bayan masu sharar ya yi nisa musamman waɗanda aka tantance su a baya, kuma za a neme su nan ba jimawa ba.

“Duk wanda ya san an tantance shi a baya, to ya tara takardunsa da za su zamo shaida yayin biyansa albashin da yake bi bashi” a cewar Garo.

Martanin na kwamishinan muhalli Nasir na biyo bayan zanga-zangar lumana da masu sharar titin suka gudanar a ranar Alhamis.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!