Labarai
NANS ta gargaɗi ƙungiyar NUPENG kan sukar matatar Mai Dangote

Kungiyar ɗaliban Najeriya NANS, ta gargadi ƙungiyar masu dakon man fetur ta NUPENG kan ta daina sukar kokarin da matatar man fetur ta Dangote ke yi wajen magance matsalolin fetur da tsadar sa da ake fuskanta.
Shugaban kungiyar na Olushola Oladoja, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai yau Juma’a a Abuja.
Ya kuma ce matatar ta Dangote na kokarin fitar da ‘yan Najeriya miliyan 200 daga kangin da suke ciki.
Oladoja ya ƙara da cewa, matatar mai ta Dangote, wadda ke da karfin tace gangar mai har 650,000 a kowace rana, ta zama wata babbar dama ga tattalin arzikin ƙasar, domin ta samar da wadatar man fetur ga cikin gida da kuma damar fitarwa zuwa ƙasashen ƙetare.
You must be logged in to post a comment Login