Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Nasarar ‘yan wasa a harkokin wasanni shi ne burin mu – Abba Yola

Published

on

Tsohon baban jami’i a hukumar ƙwallon ƙafa ta ƙasa , kana shugaban ma’aikatan Ministan wasanni na ƙasa ,Alhaji Abba Yola , ya tabbatar da cewa nasarar ‘yan wasan ƙasar nan , walau masu Lafiya ko bukata ta musamman (Nakasa ), a harkokin wasanni shi ne burin hukumomi a fadin Najeriya.

Yola , ya bayyana hakan ne ya yin da yake zantawa da manema labarai, a filin wasa na Moshood Abiola , dake birnin tarayya Abuja , wajen buɗe gasar masu buƙata ta musamman karo na farko ta ƙasa , mai taken First maiden National Para Games Abuja 2022,da zata gudana daga ranar Lahadi 10 Afrilu zuwa Asabar 16 2002.

A cewar tsohon gogaggen masani kana shugaban wasannin, yace kirkiro wannan gasar abun alfahari ne kasancewar gasa ce da ake fatan zata ɗore duba da yadda Duniya ta canja tsarin wasa ta fuskar masu buƙata ta musamman.

“Tuni Duniya ta buɗe tare da faɗaɗa wasanni daban -daban, ciki har da na masu (Nakasa), tare da wasannin motsa jiki na Bazara (Olympic) “.

“Jihohin Arewacin ƙasar nan sun ƙarbi wasannin wanda abun murna ne, kuma muna fatan gwamnatoci da kamfanoni zasu shigo don ɗabbaka lamarin , kar a barwa gwamnati ita kadai, ta hakan za’a taimakawa masu yi ta fannoni da dama ciki har da abun dogaro da kai , tare da mai da su wasu al’umma masu muhimmanci a cikin mutane” a cewar Abba Yola.

Jihohi 21 ne ake sa ran zasu fafata a wasanni daban -daban har 15, da aka ware za a fara , inda kawo yanzu jihohi 18 sun iso gasar , tare da ɗumbin ‘yan wasa masu buƙata ta musamman (Nakasa), da zasu nuna hazaka da baiwar da suke da ita.

Ministan matasa da wasanni Sunday Dare, ya ƙaddamar da gasar a Asabar 09 ga Afrilu 2022, da, za a shafe mako guda ana bugawa daga Lahadi 10 zuwa Asabar 16 ga Afrilu 2022.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!