Labarai
NASU DA SSANU sun yi barazanar gudanar da zanga – zanga a Najeriya
Kungiyar ma’aikatan jami’o’i da ba NASU malamai da hadin gwiwar kungiyar manyan malaman jami’o’ ta kasa SSANU sun yi barazanar shiga zanga-zangar kwanaki uku daga gobe Talata 12 ga watan Jnairun da muke ciki.
Hakan na cikin wata sanarwar hadin guiwa da kungiyoyin biyu suka fitar a jiya Lahadi a Abuja mai dauke da sa hannun sakatare janar na kungiyar NASU, Mista Peters Adeyemi da shugaban kungiyar SSANU, Mista Mohammed Ibrahim.
Sanarwar ta bayyana cewa, kungiyoyin biyu sun shirya gudanar da zanga-zangar ne don nuna rashin amincewarsu na rashin aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma da Gwamnatin Tarayya.
A cewarsu, sauran bukatun su ne rashin biyan kudin fansho na mambobin da suka kammala aiki, ya saba wa ka’idojin aiki da tsarin da ya kafa kungiyoyin.
A don haka kungiyoyin ke sanar da cewa, za su gudanar da zanga-zangar kwanaki uku daga Talata 12 zuwa Alhamis 14 ga watan Janairun da muke ciki a kowane reshe na kungiyar.
You must be logged in to post a comment Login