Labarai
NBA ta yi Allah-wadai da zargin jami’an DSS na sace wata yarinya a Jigawa

Kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Jigawa ta yi Allawadai da zargin da ake yiwa wani jami’in hukumar DSS na sace wata yarinya yar asalin garin Hadeja tsawon shekara biyu tare da canza mata addini.
Shugaban kungiyar a jihar Barista Hamza Garba Umar ya shaidawa Freedom Radio cewa kungiyar su za ta tabbatar da an yi adalci a wannan shari’a da zarar an kamo wadda ake zargin.
Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta bakin mai magana da yawunta SP Lawan Shisu Adam ya tabbatarwa Freedom Radio cewa sun karbi umarni daga wata Kotun majistare dake Hadeja na kamo wadda ake zargin tare da gurfanar da shi a gaban kotu.
You must be logged in to post a comment Login