Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An sake ceto ƙaramar yarinya da aka killace a Kano

Published

on

Jami’an ƴan sanda da haɗin gwiwar ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right sun ceto wata yarinya da ake zargin an ƙulle ta tun farkon shekarar nan a cikin gida, a unguwar Kuntau layin Alfindiki da ke ƙaramar hukumar Gwale a nan Kano.

Yarinyar mai suna Favour ƴar shekaru 11 ta shaida wa Freedom Radio cewa, ƙanwar mahaifiyarta ce ta ɗauko ta, tun daga jihar Taraba, kuma ta kulle ta ba tare da bata damar zuwa ko ina ba.

Wata maƙociyar gidan da abin ya faru ta ce, gidan ya jima a rufe sai dai kawai, lokaci zuwa lokaci suna ganin ana zuwa a buɗe shi.

Wakilin mu Abba Isah Muhammad ya zanta da shugaban ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network Malam Ƙaribu Yahya Lawal Kabara wanda ya ce yanzu haka yarinyar da aka ceto tana hannun ƴan sandan Ɗorayi Babba domin yin bincike.

Duk ƙoƙarin da Freedom Radio ta yi don jin ta bakin matar da ake zargi da tsare yarinyar abin ya ci tura, sakamakon ba a same ta a gida ba.

Sai ku biyo mu a nan gaba don jin ta bakinta, da ma matsayar rundunar ƴan sandan Kano a kai.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!