Kasuwanci
NBS: An samu tashin farashin kayayyaki mafi muni a Najeriya cikin shekaru 4
A rahoton farashin kayayyaki da hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta saba fitarwa na shekara-shekara, ya ce, a watan jiya na Maris, an samu tashin farashin kayayyaki mafi muni a Najeriya cikin shekaru hudu da suka gabata.
A cewar NBS farashin kayayyakin ya tashi da kaso 18.17.
Wannan adadi dai ya nuna cewa, an samu gibin 0.82 fiye da yadda farashin yake a watan shekaran jiya na Fabrairu, wanda ya tsaya akan kaso 17.33.
Rahoton hukumar kididdiga ta kasar da aka wallafa a yau alhamis, ya nuna cewa, tashin farashin kayayyakin da aka samu shine mafi muni cikin shekaru hudu da suka gabata.
A bangare guda rahoton na NBS ya kuma nuna cewa a birane an samu hauhawar farashin da kaso 18.76, ya yin da a yankunan karkara aka samu hauhawar farashin da kaso 17.60.
You must be logged in to post a comment Login