Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NBS : Gwamnati ta sami sama da biliyan 651 a matsayin kudaden shiga

Published

on

Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce gwamnatin tarayya ta samu kudaden shiga daga bangaren harajin kayayyaki wato VAT cikin watanni shida na farko na wannan shekara da suka kai naira biliyan dari shida da hamsin da daya da miliyan saba’in da bakwai.

A cikin wani rahoto da hukumar ta NBS ta wallafa a website dinta, rahoton ya nuna cewa, adadin ya zarce wanda aka tattara a wa’adi irin wannan na watanni shidan farko a shekarar da ta gabata, wanda ya tsaya akan naira biliyan dari shida da miliyan casa’in da takwas.

Rahoton ya nuna cewa, an samu karin kaso takwas da digo biyar idan aka kwatanta da na bara.

Hukumar kididdiga ta kasar ta kuma ce bangaren kwararru shine ya fi samar da kudade masu yawa da ya kai naira biliyan casa’in da biyar da miliyan casa’in da biyu, sai bangaren masana’antu da aka tattara harajin na kayayyaki da ya kai naira biliyan sittin da bakwai da miliyan sittin da uku.

Haka zalika bangaren kasuwanci ya samar da naira biliyan talatin da daya da miliyan goma, sai kuma bangaren masaku da jima da kayyakin asibiti da sabulai da sauransu da suka samar da harajin na VAT da ya kai sama da naira biliyan daya da miliyan dari biyu da saba’in da biyar

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!