Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan Najeriya sama da miliyan 10 ne ke fama da cutar Hepatitis

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce akalla al’ummar kasar nan miliyan goma sha takwas ne suke fama daga cikin nau’ikan cutar hanta wato Hepatitis.

Shugabar shirin dakile cututtuka da ake daukarsu ta saduwa ta kasa Akudo Ikpeasu ne ta bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a wani bangare na ranar yaki da cutar hanta ta duniya.

Ta ce, akwai akalla mutane miliyan goma sha shida da suke dauke da nau’in cutar ta Hepatitis B yayin da wadanda suke dauke da cutar nau’in Hepatitis C suka kai miliyan biyu da dubu dari biyu.

Misis Akudo Ikpeasu ta kuma ce, akwai bukatar yin gwaji ga dukkannin al’ummar kasar nan wanda shine babbar mataki na shawo kan yaduwar cutar.

Da ya ke gabatar da jawabi wani likita da ke rajin kawadda cutar a Najerya Dr Mike Omotosho, ya ce, akalla mutane miliyan dari biyar ne a duniya baki daya ke dauke da daya daga cikin nau’ikan cutar, yayin da miliyan daya da dubu dari hudu ke mutuwa sanadiyyar cutar a kowace shekara.

 

AI

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!