Kiwon Lafiya
NCC:wayar salula fiye da miliyan casa’in ne basu da rijistan layukansu
Hukumar kula da kafofin sadarwa ta kasa (NCC), ta ce, masu amfani da wayar salula miliyan casa’in da biyar da dubu dari bakwai ne basu da cikakken rajistar layukan wayar salular su a kasar nan.
A cewar hukumar lamarin ya faru ne sakamakon rashin daukar cikakken bayanan su ta hanyar dangwala yatsa da kuma hoton fuskar su, watakila saboda tangardar na’ura.
Hukumar NCC ta kuma ce, nan gaba ba da dadewa ba, za ta aika da sakon text ga masu wadannan layukan tarho da su je su yi cikakken rajistar layukansu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar jiya a Abuja wanda aka rabawa manema labarai.
Sanarwar ta ce, kwamishina mai kula da harkokin masu ruwa da tsaki a hukumar Mr. Sunday Dare ne ya bayyana haka, yayin wani taron karawa juna sani a garin Fatakwal babban birnin jihar Rivers.