Manyan Labarai
NDDC ta bayyana masu karbar kwangila a hannun ta – Majalisa
Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya baiwa shugaban hukumar da ke kula da yankin Niger Delta Godswill Akpabio wa’adin kwanaki biyu da ya bayyanawa majalisar sunayen ‘yan majalisar da suka karbi kwangila a hannun hukumar.
A jiya ne dai Akpabio ya bayyanawa kwamitin da ke binciken hukumar da almundahanar kudade cewa, kaso 60 na kwangilar da hukumar ke bayarwa tana zuwa hannun ‘yan majalisar ne.
Sai dai tuni gwamnatin tarayya ta kafa kwamitin da zai binciki hukumar kan zargin almundahanar kudade da yawan su ya aki Naira biliyan tamanin da daya.
Ta cikin jawabin da shugaban majalisar Femi Gbajabiamila yayi a yau Talata, ya ce tun bayan da ya karbi shugabancin majalisar a shekarar 2003 bai taba karbar kwangila a hannun hukumar ta NDDC ba har kawo yanzu.
A don haka ne Gbajabiamila yace daga yanzu ya baiwa hukumar wa’adin awanni 24 zuwa 48 da ya gabatarwa da majalisar sunayen ‘yan majalisun da suke karbar kwangila a hannun hukumar NDDC da ya kai kaso 60 na kwangilar da hukumar ke aiwatarwa don tattara bayanai.
You must be logged in to post a comment Login