Labarai
NDLEA ta kama kasurgumin dillalin hodar Ibilis a Sokoto
Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa a jihar Sokoto sun kama wani gawurtaccen dillalin kwaya dauke da hodar iblis wato cocaine da kudinta ya kai naira biliyan daya.
Mutumin mai suna Nkem Timothy mazaunin kasar Algeria ya canja sunansa zuwa Auwalu Audu da nufin yin badda kama don safarar kwayar ba tare da an gano shi ba.
Hakan na cikin wata sanarwar ce mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na hukumar ta NDLEA Femi Babafemi.
Rahotanni sun ce jami’an hukumar ta NDLEA sun kama Timothy ne mai shekaru 36 wanda ke kokarin safafar hodar iblis din ta kasar jamhuriyar Nijar zuwa kasar Algeria.
An kuma kamashi dauke da daurin hodar iblis guda sittin da biyu wanda ya dauresu cikin robar madaran yoghurt.
You must be logged in to post a comment Login