Connect with us

Labarai

NDLEA ta kama wanda ake zargi da safarar hodar Iblis a Kano

Published

on

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa, NDLEA, ta cafke wani dan kasuwa dan shekara 62 mai suna Nwabueze Izueke a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano da ke jihar Kano, bisa zargin yunkurin safarar hodar iblis zuwa kasar China.

 

Bayanin da kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya fitar ya nuna cewa an kama Izueke ne a ranar 31 ga Janairu, 2026, yayin tantance fasinjojin da ke shirin tafiya zuwa China ta Addis Ababa a jirgin Ethiopian Airlines. Gwajin binciken jiki da aka masa ya tabbatar da cewa ya hadiye miyagun kwayoyi.

 

A yayin sa ido a kansa, wanda ake zargin ya fitar da kwantena 95 na hodar iblis, masu nauyin kilogiram 1.589. Ya bayyana cewa shi dan kasuwa ne a Legas, kuma ya shiga safarar kwayoyin ne domin tara kudin kammala ginin gida a kauyensu Iwollo da ke jihar Enugu.

 

NDLEA ta ce wannan kamen na daga cikin jerin manyan ayyukanta na kwace miyagun kwayoyi da kuma cafke masu safararsu a sassan kasar nan daban-daban, domin dakile yaduwar shaye-shaye da fataucin kwayoyi a Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!