Labarai
NDLEA ta kama wani ɗan kasuwa da ya hadiye Cocain 127 a cikinsa a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano

Hukumar NDLEA ta kama wani ɗan kasuwa mai suna Ejiofor Godwin Emeka, ɗan shekara 52, a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano bayan gano kullin 127 na cocaine da ya haɗiye .
Emeka yaa iso daga Bangkok, Thailand, ta jirgin Ethiopian Airlines, inda bincike ya nuna ya haɗiye ƙwayoyi masu hatsari kafin dawowarsa ƙasar.
A Legas, jami’an NDLEA sun kuma kama wasu kaya da ake shirin tura su ƙasashen waje — ciki har da Birtaniya, Australia, Turkiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), da Afirka ta Kudu. Miyagun ƙwayoyin da aka gano sun haɗa da methamphetamine, tramadol, cocaine, da skunk, waɗanda aka ɓoye cikin kayan ado, kwalaben giya, jakunkunan mata, da sabulun wanka domin kaucewa gano su.
A wasu jihohi kamar Edo, Osun, Rivers, Katsina, Niger, Ondo, da Kaduna, hukumar ta gudanar da jerin sama da dubban kama inda ta kwace fiye da kilo 1,000 na miyagun ƙwayoyi da ta kama da masu safararsu.
Shugaban hukumar, Janar mai ritaya Buba Marwa, ya jinjinawa jami’an NDLEA bisa jajircewa da ƙwarewa wajen ci gaba da yaki da shan da fataucin miyagun ƙwayoyi a faɗin Najeriya, tare da kira garesu da su ci gaba da gudanar da aikinsu da gaskiya da himma.
You must be logged in to post a comment Login