Connect with us

Labarai

Neja: Yan sanda sun kama mutane 6 da ake zargi da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba

Published

on

Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kama wasu masu mutane 6 masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a wani wurin da ake hakar ma’adanai da ke kauyen Dangado a karamar hukumar Paikoro a jihar. 

 

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda a jihar, Wasiu Abiodun, ya ce kamen ya biyo bayan samun  sahihan bayanai, na sirri.

 

Abiodun ya ce rundunar ‘yansandan ta ta kai farmaki wurin da ake hakar ma’adinan inda suka yi artabu da masu hakan ma’adanai da ke dauke da muggan makamai.

 

A yayin samamen, kakakin ‘yansandan na  Neja ya ce an kama mutane shida a wurin da ake hakar ma’adinan yayin da wasu kuma suka tsere.

 

Abiodun ya bayyana sunayen wadanda ake cafken da Aliyu Rabiu, Samaila Ibrahim, Sadiku Auwal, Ibrahim Babangida, Musa Adamu da Sani Hassan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!