Kimiyya
NEMA : Za’a fuskanci ambaliyar ruwa a wasu jihohin Arewa
Hukumar bada Agajin gaggawa ta kasa NEMA ta bukaci mazauna jihohin Zamfara da Sokoto da Kebbi da su kaucewa zubar da shara barkatai domin gujewa afkuwar ambaliyar ruwa da take barazana ga jihohinsu.
Babban darakta a hukumar Muhammad Alhaji Muhammad ne ya bayyana hakan yayin taron gangamin wayar da kai da hukumar ta shirya da hadin gwiwar gwamnatin jihar Zamfara.
A cewarsa sakamakon yawan ruwan sama da ake samu yasa hukumar ta ga dacewar shirya gangamin domin wayar da kan al’umma akan mahimmacin tsaftar muhalli da kuma amfanin yashe magudanan Ruwa.
Da yake jawabi kwamishinan muhalli a jihar ta Zamfara, Dakta Nuraddeen Isah, ya ce, wayar da kan al’ummar jihar zai taimaka sosai wajen magance matsalar ambaliyar ruwa dake barazana ga jihar.
You must be logged in to post a comment Login