Connect with us

Kiwon Lafiya

NEMA:gwamnatin tarayya ta kai dauki ga al’ummar jihohin Adamawa da Taraba

Published

on

Hukumar agajin gaggawa ta kasa NEMA ta bukaci gwamnatin tarraya da ta kai dauki ga al’ummar jihohin Adamawa da Taraba, sakamakon rikicin ‘yan-tada kayar baya da rikicin kabilanci.

Babban darakta na hukumar Akube Iyawu ne ya bayyana haka, yayin zantawa da manema labarai, a babban birnin Yola na jihar Adamawa.

Akube Iyawu ya kuma ce, sun zo Jihar ne don ganiwa idanun su barnar da jihohin biyu suka samu sakamakon tashe-tahsen hankalin a sassan Jihohin.

Akube Iyawu ya kuma ce, al’ummar jihohin na bukatar agajin don kuwa yawancin su, sun rasa dokiyoyinsu da dama, hadi da matsugun-nansu  baya ga rashin zaman lafiya da ke adabar jihohin

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,340 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!