Labarai
NFIU ta haramtawa bankuna hada-hada ta cikin asusun hadaka tsakanin kananan hukumomi da jihohi
Sashen kula da bayanan sirri kan harkokin kudi wato Nigerian Financial Intelligence Unit NFIU, ya haramtawa bankunan Najeriya gudanar da hada-hada ta cikin asusun hadaka tsakanin kananan hukumomi da jihohi ba tare da kudaden sun shiga asusun ajiya na kananan hukumomin ba.
Masana harkokin kudi dai na cewa lamarin ya kawo karshen taba kudaden kananan hukumomi da gwamnonin jihohi ke yi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun sashen na NFIU Ahmed Dikko.
A cewar sanarwar, daga ranar 1 ga watan Yunin wannan shekara duk wani bankin da ya karya ka’idar da sashen ya saka, to kuwa ba shakka za a dauki tsas-tsauran matakin ladaftarwa a kansa, wanda zai shafi harkokin sa a nan gida Najeriya dama kasashen ketare.
Sanarwar ta kuma ce tuni aka mikawa babban bankin kasa CBN da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na kasa EFCC da ICPC ka’idoji kan sarrafa kudaden kananan hukumomin don sa ido kan lamarin.
Haka kuma sanarwar ta ce, dokar hadakar asusun ajiya na kananan hukumomi da jihohi, ya bukaci amfani da kudaden ne kawai a kananan hukumomin da aka turo da domin su, a don haka sashen ba zai taba lamunta ba wani mutum ya karkatar da kudaden zuwa wani yanki ko wani aiki da banan aka turo da kudin ba.
Bugu da kari hukumar ta kuma ce babu wata karamar hukumar da za ta cire sama da naira dubu dari biyar daga asusun ajiyar a rana guda.