Labarai
NGF ta bukaci jagororin Plateau su dauki matakan dakatar da kashe-kashe a jihar

Kungiyar Gwamnonin Najeriya, ta buƙaci jagororin jihar Plateau da su haɗa kan al’ummar jihar domin dakatar da kashe-kashen mutane da ake yawan samu.
Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan jihar Kwara Abdulrahman Abdulrazaq, ne ya bukaci hakan da yammcin ranar Alhamis lokacin da ya kai ziyarar jaje jihar.
Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq, ya kuma bukaci masu fada aji da duk masu ruwa da tsaki a jihar da su haɗa hannu waje guda don dawo da zaman lafiya a jihar
Rahotanni sun bayyana cewa fiye da mutune 100 aka kashe cikin makonni biyu da suka gabata, lokacin da wasu mahara suka kai hari wasu garuruwa da ke yankin ƙananan hukumomin Bokkos da Bassa a jihar.
You must be logged in to post a comment Login