Labarai
Nijar: Dakarun Garde Nationale sun cafke mutane shida da ake zargi da safarar fetur ga yan ta’adda

Wani samame da rundunar tsaron Nijar ta Garde Nationale ta gudanar ya bata damar kama wasu mutane shida da ake zargi da safarar man fetur ga kungiyoyi masu ɗauke da makamai.
An kama mutane shida da ake zargi ne a wani ɓangare na ayyukan da rundunar ta ƙaddamar cikin ƴan kwanakin nan domin yaki da ta’addanci da safarar man fetur da ake yi wa ƙungiyoyi masu tayar da ƙayar baya.
Jamhuriyar Nijar dai na fuskantar barazanar tsaro daga mayaƙa masu riƙe da bindiga, a daidai lokacin da ƙasar ke ci gaba da kasancewa a ƙarƙashin mulkin soji.
You must be logged in to post a comment Login