Connect with us

Labarai

NIMET: Akwai yiwuwar sake ambaliyar ruwa nan da kwanaki uku masu zuwa

Published

on

Hukumar lura da yanayi ta ƙasa NIMET, ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar sake samun ambaliyar ruwa nan da kwanaki uku masu zuwa.

A wata sanarwa da ta fitar ranar Talata, hukumar ta ce, ana fargabar samun ambaliyar a wasu jihohi 32 na ƙasar nan.

Daga cikin jihohin sun haɗa da Kano da Jigawa da Kaduna da Bauchi, sai kuma jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Sai jihohin Gombe da Yobe da Filato da jihar Adamawa da Taraba, sai kuma birinin tarayya Abuja da kuma ƙarin wasu jihohi 17.
Hukumar ta kuma yi kira ga mutane, da su tsaftace magudanan ruwa don kaucewa ambaliyar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!