Labarai
NIMET ta yi hasashen yin Hazo da Kura na kwanaki 3
Hukumar hasashen yanayi ta kasa NIMET, ta yi hasashen cewa za a fuskanci yanayin hazo da kura a sassan kasar nan daga yau Litinin zuwa jibi Laraba.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar ta ce, yankunan Arewacin kasar nan da dama ne za su fi fuskantar yanayin na hazo da kura.
Haka kuma, NIMET, ta kara da cewa, ce za a samu matsala wajen hangen nesa saboda hazon a tsawon wadannan kwanaki.
Hukumar ta bukaci al’ummar da ke zaune a yankunan da hazon zai fi yin kamarai da su dauki matakan kariya musamman wadanda ke fama da wata lalura da ta shafi rashin kura ko hazo kamar Asma ko kuma cutukan da suka shafi numfashi.
You must be logged in to post a comment Login