Labarai
Nimet tace akwai hasashen samun mamakon ruwan sama Awasu jihohin Arewa
Hukumar Kula da Yanayi ta kasa (NIMET) ta ankarar da wasu mazauna jihohin arewa kan su shirya wa mamakon ruwan sama a ƴan kwanaki masu zuwa.
A cewar sanarwar da aka fitar a jiya Alhamis, ana ganin gangamowar hadari a wasu sassan arewacin ƙasar nan ciki har da Borno da Taraba da Gombe da Bauchi da kuma Kano, inda ake tsammanin hadarin zai yaɗu zuwa yammacin kasar.
Sanarwar ta ƙara da cewa hadarin da ake fuskanta ana sa ran zai kai ga gabashin ƙasar haɗe da iska a jihohin Plateau da Nasrawa da Jigawa da Adamawa da Yobe da Borno da Bauchi da Gombe da Kaduna da Kano da kuma Katsina.
NIMET ta kuma ce yankunan da ake tsammanin hadari, akwai yiwuwar a yi iska mai ƙarfi da ake sammanin zai zo da ruwan sama, da ka iya lalata bishiyoyi da turakun wutar lantarki da gine-gine masu rauni.
You must be logged in to post a comment Login