Labarai
NLC ta gargaɗi Gwamnatin tarayya kan yajin aikin ASUU
Kungiyar Ƙwadago ta kasa NLC ta gargaɗi gwamnatin tarayya kan ta daina barazanar yin amfani da manufar “ba aiki, ba albashi” kan yajin aikin kungiyar malaman jami’o’imalaman jami’a ASUU.
Shugaban kungiyar ta NLC Joe Ajaero ne ya bayyana hakan a zantawarsada manema labarai.
Ajaero ya ce, gwamnati ta yi amfani da wa’adin makonni biyu da ASUU ta bayar wajen warware matsalolin da ke tsakaninsu, maimakon tsoratar da malamai. Ya bayyana cewa yajin aikin ASUU ba na malaman jami’a kaɗai ba ne, amma gwagwarmaya ce don kare makomar ilimin jama’a a Najeriya.
Ya ƙara da cewa wannan barazana ta “ba aiki, ba albashi” tana ƙara nuna bambancin tsakanin ‘ya’yan talakawa da na masu kuɗi da ke karatu a ƙasashen waje.
NLC ta ce idan bayan makonni biyu gwamnati ta kasa warware matsalar, za ta haɗa kai da ASUU da sauran ƙungiyoyin ma’aikata don tsayar da tattalin arzikin ƙasar, domin kare ilimin jama’a da tabbatar da adalci ga malamai.

You must be logged in to post a comment Login