Labarai
NNPP ta nemi INEC ta sanya sahihin tambarinta a takardun zabe

Jam’iyyar NNPP ta bukaci hukumar zabe mai zaman kanta INEC da ta dakatar da dukkan zabukan har sai an sanya sahihin tambarinta a kan takardun kada kuri’a.
A cikin wata takarda da lauyan jam’iyyar, Mista Ndubuisi Ukpai, ya aike wa INEC, NNPP ta bayyana cewa hukumar ta gaza bin hukuncin kotu da ke tabbatar da sahihancin shugabancin jam’iyyar karkashin Dakta Major Agbo.
Takardar, wadda aka aike wa INEC a ranar 25 ga Agusta, 2025, ta bukaci a dakatar da duk wani zabe har sai an gyara tambarin jam’iyyar a takardun kada kuri’a, tare da tabbatar da sahihancin shugabancinta
A baya, jam’iyyar NNPP ta koka kan yadda INEC ta yi amfani da tambarin jam’iyyar da ba a iya ganewa a takardun zabe, wanda ya janyo rudani ga masu kada kuri’a da kuma rasa kuri’u.
A wasu jihohi irin su Anambra da Oyo, jam’iyyar ta bukaci a soke zabubbukan da aka gudanar saboda wannan matsala.
Jam’iyyar NNPP na ci gaba da neman adalci ta hanyar kotu, tare da bukatar a gyara wannan kuskure kafin ci gaba da gudanar da zabubbuka a kasar.
You must be logged in to post a comment Login