Kasuwanci
NPA ta bukaci masu son fitar da kayayyaki su rika ziyartar shafinta don samun bayanai

Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwan kasar nan NPA ta ce damar makin da Najeriya ke da su a birnin tarayya Abuja na bunkasa harkokin Noma da Masana’antu sun zama ginshiƙi wajen ƙarfafa manufar gwamnatin tarayya ta bunƙasa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga ba tare da yin la’akari da arzikin man fetur ba.
Shugaban Hukumar Dakta Abubakar Dantsoho, ne ya bayyana hakan, yayin bikin baje kolin kasuwanci na kasa da kasa da ke gudana a Abuja da hukumar ta NPA ta shirya.
Dantsoho ya ce hukumar ta samar da Cibiyoyin Sarrafa Kayayyakin Fitarwa domin sauƙaƙa duk wasu matakai na fitar da kayayyaki daga kasar nan, ta yadda za a gujewa tsaikon da ake samu a kasuwannin Duniya.
Dantsoho ya ƙara da cewa hukumar tana aiki kan tsarin Ports Community System (PCS) da kuma National Single Window (NSW) da zai haɗa duk masu ruwa da tsaki a fannin kasuwanci a rukuni daya da yai dai-dai da zamani, don magance jinkiri da kawar da matsalolin kasuwanci.
Hukumar tashoshin jiragen ruwan ta kuma roƙi ‘yan kasuwa da masu saka hannun jari kan su yi amfani da sauƙaƙan hanyoyin fitar da kaya, tare da ziyartar shafin hukumar a kan www.nigerianports.gov.ng domin samun dukkan bayanan da ake buƙata.
You must be logged in to post a comment Login