Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

NPFL: Kano Pillars ta yi rashin nasara a hannun Katsina United

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi rashin nasara a wasan hamayya da ta buga da Katsina United a gasar firimiya mako na uku da ci 1-0. 

Wasan ya gudana a yau Alhamis 30 ga Disambar 2021 a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke jihar Katsina.

Tun da fari dan wasa Abba Umar ne ya zura kwallo daya dilo a minti na 3 da wasan.

Kano Pillars dai a wasanni uku da ta buga maki daya kacal ta samu.

Da kawo yanzu ita ce ta karshe wato ta 20 a gasar ta Firimiya bayan fafata wasanni uku a sabuwar kakar wasannin 2021/2022.

Yayinda Kano Pillars zata kece raini a wasan hamayya na gaba da Enyimba a ranar biyu ga watan Janairun sabuwar shekara mai kamawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!