Connect with us

Labaran Wasanni

NFF ta nada sabon mai horar da kungiyar Super Eagles

Published

on

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya NFF ta nada Jose Peseiro a matsayin sabon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta kasar Super Eagles.

Hukumar ta NFF ta sanar da hakan ne a ranar Laraba 29 ga watan Disambar shekarar da muke ciki ta 2021.

Jose Peseiro shine zai maye gurbin tsohon mai horar da tawar ta Super Eagles Gernot Rohr da aka sallama bayan da ya shafe shekaru biyar yana jagorantar ta.

Kafin nadin nasa Najeriya dai ta nada tsohon dan wasan kasar Augustine Eguavoen a matsayin mai horarwa na rikon kwarya.

Augustine Eguavoen da kawo yanzu tuni ya fitar da jerin sunayen ‘yan wasa 28 da za su wakilci Najeriya a gasar cin kofin kwallon kafar Afrika da za a gudanar a kasar Kamaru a shekara ta 2022 mai kamawa.

Zuwa yanzu ana saran sabon mai horar da kungiyar Jose zai fara shirin tin karar gasar ta AFCON da za ta fara gudana daga ranar 9 ga watan Janairun 2021.

Sabon mai horarwar dan kasar Portugal  ya kuma yi fatan kai Najeriya zuwa gasar cin kofin Duniya da za a gudanar a kasar Qatar a shekara ta 2022.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!