Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

NPFL: Niger Tornadoes da Gombe United Sun dawo gasar

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Niger Tornadoes da Gombe United sun samu nasarar dawowa gasar Firimiya ta Najeriya wato NPFL.

Kungiyoyin 2 sun samu nasarar ne bayan da sukai kunnan doki tsakanin su a wasan da suka fafata a yau Asabar 11 ga watan Satumbar shekarar 2021.

Wasan dai an bugashi a jihar Enugu.

Tornadoes ta kammala rukunin da taka na A a matsayin ta 1 da maki 5 bayan nasarar da ta yi a wasa 1 da kuma kunnan Doki wasanni 2 cikin wasanni 3 data buga.

Yayin da ita kuma Gombe United ta kammala a mataki na 2 itama da maki 5 sai dai akwai banbancin kwallaye tsakanin ta da Tornadoes.

A gefe guda kuma kungiyar kwallon kafa ta
El-kanemi Warriors, ta gaza samun buga gasar ta NPFL da itama ke rukunin na A.

Kungiyar da ke garin Maiduguri dai ta kammala a mataki na uku a rukunin da maki 4.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!