Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

NPLF: Kano Pillars ta doke Niger Tornadoes

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi nasarar doke takwararta ta Niger Tornadoes Fc da ci daya mai ban haushi a gasar firimiya ta kasa NPFL.

Fafatawar da ta gudana a filin wasa na Ahmad Bello da ke Kaduna a ranar Lahadi 16 ga Janairun 2022.

Dan wasa Mark Daniel ne ya zura kwallon, bayan samun taimakon daga hannun Yusuf Maigoro a minti na 49 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Kawo yanzu Kano Pillars na mataki na 11 da maki 7 a wasanni shida da ta buga a kakar wasannin shekarar 2021/2022 da muke ciki.

A sauran wasannin da aka buga Akwa United 2-0 Katsina United.

Gombe United 0-0 Enyimba

Shooting Stars 2-2 Sunshine Stars

Plateau United 5-0 Dakkada

Kano Pillars 1-0 Niger Tornadoes

Rivers United 3-0 Kwara Utd

Abia Warriors 1-0 Heartland

Nasarawa United 2-1 Lobi Stars

Rangers 2-0 MFM

Wikki tourists 1-2 Remo Stars.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!