Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

NUJ ta nemi shugabanni su jajirce wajen kare haƙƙoƙin ma’aikata

Published

on

Ƙungiyar ƴan jarida ta kasa reshen jihar Kano ta ce, za ta ci gaba da kare mutuncin ƴan jarida a kowanne mataki, baya ga ƙarfafa musu gwiwa don gudanar da ayyukan su yadda ya kamata.

Shugaban ƙungiyar reshen Jihar Kano Kwamared Abbas Ibrahim ne ya bayyana hakan yayin rantsar da sababbin shugabannin ƙungiyar na tashar Freedom Radio a yau Laraba.

Kwamaret Abbas ya buƙaci sabbin shugabannin da su yi aiki tuƙuru da kiyaye haƙƙoƙin ma’aikata hadi da ƙara ƙaimi wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.

Da take jawabi, sabuwar shugabar ƙungiyar Kwamaret Aisha Muhammad Ƴalleman ta ce, za suyi aiki tuƙuru, tare da kawo ci gaba ga ma’aikatan Freedom Radio.

Daga cikin waɗanda aka rantsar a yau, akwai Kwamared Aisha Muhammad Yalleman a matsayin shugabar Kungiyar sai Abdullahi Isa a matsayin mataimakin shugaba sai Muzammil Ibrahim Yakasai a matsayin Sakatare.

Sauran sune Abdulkarim Muhammad Abdulkarim a matsayin mataimakin sakatare, sai Adamu Sulaiman Muhammad a matsayin mai binciken kuɗi sai kuma Shamsiyya Farouk Bello a matsayin ma’ajin kungiyar, da kuma Tijjani adamu a matsayin Odita.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!