Kiwon Lafiya
NUPENG:shugaba Buhari da ya kauracewa shawarwarin da zai rikita tattalin arzikin kasa
Ma’aikatan a bangarin man fetur da isakar gas sun shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya kaucewa dukkanin shawarwarin da za’a bas hi wanda ka iya hautsinawa ko tada rikici ga tattalin arzikin kasar nan.
Wannan na kunshe cikin sanarwar da Kungiyar ma’aikatan man fetur da isakar gas ta kasa NUPENG da kuma kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da isakar gas ta kasa PENGASSAN suka fitar a birnin Lagos.
Sanarwar mai dauke da sa hannun babban sakataren kungiyar PENGASSAN Okugbawa Lumumba da kuma babban sakataren kungiyar NUPENG Afolabi Olawale.
A dai ranar 12 ga watan nan da muke ciki na Afirilu babbar manajar darktan asusun lamuni ta duniya Chirstine Lagarde ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta cire tallafin man fetur ta dake bayar wa akan man fetur, kasancewar ana samun karancin kudaden shiga na kayyakin da ake sarrfawa a cikin gida.
Akan haka ne kungiyoyin na PENGASSAN da NUPENGA suka ce shawarar da asusun Lamunin na duniya ya bayar ya sanya fargaba a zukatan ‘yan Najeriya yayin da masu gidajen man fetur suka shiga boyewa, ganin za’a sami kari akan firashin man fetur