Labarai
Nyesom Wike ya caccaki gwamna Bala Mohammed

Ministan Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya caccaki gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, kan abin da ya kira rawar kafa, yayin da rikici ke ci gaba da addabar jam’iyyar PDP.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnan ya bayyana shirin ficewa daga PDP zuwa jam’iyyar ADC, sakamakon gazawar yunkurin sasanta rikicin cikin gida.
Jaridar Punch ta ruwaito gwamnan ya ce a baya sun tattauna yiwuwar komawa APC, amma sun fahimci ba a maraba da su a jam’iyyar, lamarin da ya sa suke shawarar shiga ADC, duk da ziyarar da shugaban Jam’iyyar na kasa Farfesa Nantawe Yilwatda, da Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf suka yi a baya baya nan.
You must be logged in to post a comment Login