Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

OIC ta bukaci Tinubu ya yi gudanar da abubuwan da suka dace

Published

on

Kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta OIC, ta bayyana nasarar da sabon zababben shugaban kasa a Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya samu a matsayin manuniya ga amincewa da al’ummar Nijeriya suka yi da manufofinsa na ci gaban kasa. 

 

Shugaban kungiyar Hissein Brahim Taha, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na kungiyar Wajdi Sindi ya sanya wa hannu.

 

Ta cikin sanarwar Hissein Brahim Taha ya jaddada muhimmancin da kungiyar ta OIC ke bai wa huldarta da Nijeriya inda ya tabbatarwa da sabon zababben shugaban kasan kudurin kungiyar OIC na bunkasa dangantaka da hulda ta kowanne fanni, musamman ma bangaren tattalin arziki da zamantakewa da kuma yaki da ta’addanci da tsauraran akidu.

 

Shugaban ya kuma yi wa Tinubu fatan samun nasara a ayyukan da ke gabansa, tare da fatan samun hadin kai da ci gaba a fadin Nijeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!