Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Pantami ya bayyana rashin jin dadinsa ga wasu jihohi na Karin kudi shinfida kayayyakin sadarwa akan tituna

Published

on

Pantami ya bayyana rashin jin dadi ga jihohin da suka kara kudin shimfida kayayyakin sadarwa.

Gwamnatin tarayya ta bayyana rashin jin dadinta dangane da shawarar da wasu jihohi suka dauka dangane da karin farashin shimfida kayayyakin ayyukan sadarwa a kan tituna biyo bayan shawarar da majalisar tattalin arziki kasa ta yanke.

Jaridar Kano Focus ta rawaito cewar jihohi 14 da suka hadar da Kano da Lagos da Anambra da Imo da Kebbi da jihar Gombe ne suka kara farashi don samar da kayayyakin ayyukan sadarwa.

Ko da yake hauhawar farashin shimfida kayayyakin sadarwa kan hanyoyi a manyan tituna gwamnatin tarayya na farawa ne daga naira dari da arbain da biyu akan kowacce mita , yayin da wasu jihohin ke bayarwa akan naira dari uku zuwa naira dari biyar akan kowanne mita wasu kuwa daga naira dari uku zuwa naira dari shida a kan kowacce mita.

Wannan Karin kuwa a mafi yawa yana ta’allaka ne ko karkashin hukumar tsara birane ta jihar kano.

Hakan ce ta sa wasu daga cikin kamfanonin layukan wayoyi suka alakanta rashin samar da layuka mai kyau da kwastamomi ke fuskanta a yanzu haka, tare da matsala ta rashin amincewa da wasu gwamnatocin jihohi suke yin na baiwa kamfanonin lasisin shimfida layukan a jihohinsu.

Wannan na daya daga cikin abubuwan da ya janyo matsalolin da kwastamomi ke fusknata a yayin da suke waya kwatsam sai layi ya katse ko samun jinkiri ko aika sako yaki tafiya da ma wasu matsalolin da suke fuskanta.

A wata sanarwa da ministan sadarwa da cigaban tattalin fasahar Sadarwa Dr Isa Ali Pantami ya fitar a jiya ya ja hankalin gwamnaoni mussammam wadanda suka bayyanawa alummarsu hukuncin da su ka yanke na basu damar gudanar da cajin shimfida layukan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!